Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jiya Wata Mota Ta Afkawa Masu Tafiya A Toronto Ta Hallaka Mutane 10


Dan sanda na tsaye kusa da gawar daya daga cikin wadanda motar ta kashe

Yan sandan Canada sun kama wani matukin wata motar da ta afkawa masu tafiya da sawu a jiya Litinin a birnin Toronto ya kashe mutane goma kana ya raunata wasu 15


Yan sandan sun ce sunan matukin Alek Minassian, amma kuma basu yi wani karin bayani a kansa ba. Sai dai kampanin yada labarai na Canada wato CBC ya rawaito jami’an gwamnati na cewar direban ba shi da wata alaka da wata kungiyar ta’addanci kana bai kasance wata barazana ga tsaron Canada.

Firayi Ministan Canada Justin Trudeau, ya jajantawa wadanda harin ya rutsa da su kuma ya mika godiya ga 'yan kwana-kwana wadanda suka fara kai dauki a inda abin ya faru.


Awata sabuwa kuma a jiya Litinin yan sanda a jahar Tennesse dake nan Amurka sun kama Travis Reinking, wanda ya harbe mutqne 6 a wani gidan cin bsnci, kamin daga bisani ya gudu.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG