Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

John Bolton Ya Zama Mai Baiwa Shugaban Amurka Shawara Akan Harkokin Tsaro


John Bolton a hannun hagu da wanda ya gada Janar H,R, McMaster
John Bolton a hannun hagu da wanda ya gada Janar H,R, McMaster

John Bolton mai ra'ayin mazan jiya, tsohon jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya wanda yake da rajin kaiwa Korea ta Arewa hari da Iran, rikakken makiyin Rasha shi ne zai zama mai ba shugaba Trump shawara akan harkokin tsaron kasa

Garanbawul da shugaban Amurka Donald Trump ke yi a fadar White House yana ci gaba, inda shugaban ya sanar da maye gurbin mai bashi shawara a kan harkokin tsaron kasa HR McMaster, da tsohon jakadan Amurka a Majalisar Dinkin Duniya John Bolton.
A wani sakon Tweeter da ya fitar da maraicen jiya Alhamis, Trump ya godewa Janar H.R. McMaster a kan irin kyakywan ayyukansa, ya ce McMaster zai ci gaba da zama abokinsa.
Kamin nadinsa, Bolton yana sharhi ne a tashar telbijin ta Fox. Ya shahara wurin a zaman mai ra'yin mazan jiya, inda yake goyon bayan amfani da karfin soji a kan Iran da Korea ta Arewa, kuma rikakken mai adawa ne ga kasar Rasha.

A wata sabuwa kuma, manyan Atoni janar na gundumar Colombia nan Washington, da makwabciyarta Maryland, sun baiwa shugaban Amurka Donald Trump takardan sammaci, bisa zargin cewa harkokin kasuwancinsa suna karo da tsarin mulkin Amurka.
A farko wannan mako ne aka baiwa Trump takardan sammacin, a matsayinsa na jami’i da kuma matsayinsa na dan kasa.


Ana kuma zargin cewa kasuwancin yankin na huskantar matsaloli saboda muhimman baki da suke shigowa yankin, za su gwammace su sauka a O'tel na Trump, don saboda su samun wata alfarma daga shugaban kasar.
Lauyoyin Trump suna da makwanni uku su amsa sammacin da aka basu.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG