Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Johnson Ya Bukaci Karin Lokacin Ficewar Burtaniya Daga EU.


Firaminista Boris Johnson

Daga baya dai, Firiministan Burtaniya Boris Johnson, ya ko aika ma kungiyar Tarayyar Turai takardar bukatar jinkirta ficewar Burtaniya daga kungiyar, da kuma wata wasika ta nuna illar tsawaita wa’adin ficewar, a cewar jaridar Associated Press.
Amma da farko, kafar labarai ta Reuters ta ruwaito cewa, Firaministan Burtaniya Boris Johnson mai kokarin dagewa kan bakarsa, ya ce shi ba zai sake shiga tattauwa ta bukatar kara jinkirta ficewar Burtaniya daga Tarayyar Turai ba, bayan da ya rasa kuri’ar da ya ke bukata a Majalisar Dokokin kasar jiya Asabar, wanda ke nufin ya wajaba a gareshi ya bukaci jinkirta ficewar.
Wannan matakin da Majalisar ta dauka, a ranar da Johnson ya ayyana a zaman rana mai matukar tasiri ga makomar Burtaniya, ya kara yiwuwar a samu jinkiri a shirin ficewar, wanda hakan kuma ka iya kara bayar da dama ga masu adawa da shirin ficewar da ake wa lakabi da Brexit, su yi kafar ungulu ga ficewar da Burataniya ke shirin yi.

Majalisar ta kada kuri’u 322 akasin 306, na bukatar wata gyara ta kalmomi 26, wanda hakan ya sa ya zama dole Firaministan ya bukaci Tarayyar Turai ta amince da jinkirta ficewar zuwa karshen watan Janairun badi.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG