Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Jonathan ko Buhari Babu Wanda Zai Yi Mulkin Najeriya da Sharia-inji Mafindi


Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan

Wannan makon shugaa Jonathan ke neman kaddamara da neman zabe a arewa maso yammacin Najeriya yankin dake zama mahaifar Janaral Buhari dan takarar jam'iyyar APC.

A yankin arewa maso yamma APC tana da gwamnoni uku cikinsu kuwa har da Kano, jihar da tafi kowace jiha kuri'u a Najeriya.

Inji Isa Tafida Mafindi mataimakin daraktan yada labaru na kemfen din Jonathan, idan dai ba butulci mutanen yankin zasu yi ba, yakamata su zabi shugaba Jonathan. Yace duk tsoratarwa da suke yiwa mutane na cewa shugaban kasar ba shugaba ne na addini ba yana son mutane su gane cewa babu wani shugaba da zai yi mulki da Shari'a.

Jonathan da Buhari kowanensu ya samu mulki da kundun tsarin mulkin kasar zai yi anfani dashi ba Shari'a ba. Yayi kashedin kada a yiwa mutane yaudara. Yace kowa ya sani Jonathan bai taba canza niyar tafiya da dan arewa maso yama ba wato Namadi Sambo.

Babu wanda ya taba mulkin Najeriya har ya ba yanki guda shugaban 'yansanda, shugaban kwastan, mataimakin shugaban kasa, ministan tsaro da mai bada shawara a harkokin tsaro da wasu kuma sai Jonathan.

Ga rahoto.

please wait

No media source currently available

0:00 0:01:21 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG