Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Julian Assange Ya Bayyana a Gaban Kotu


Zanen Julian Assange a gaban kotu a wata Fabrairun da ta gabata
Zanen Julian Assange a gaban kotu a wata Fabrairun da ta gabata

Lauyoyin mutumin nan da ya kirkiro kafar kwarmata bayanan sirri ta Wikileaks Julian Assange, da lauyoyin gwamnatin Amurka, sun buga muhawara a wata kotun birnin London a yau dinnan Litinin.

Wannan dai ya kasance muhimmiyar shari’ar nan ta bukatar tasa keyarsa, wadda annobar corona ta kawo jinkirin yi.

Assange, wanda ya shafe kusan shekara guda da rabi a fursunan Burtaniya, ya zauna cikin makebar wanda ake tuhuma a kotun Old Bailey, inda ya ki yadda da bukatar Amurka ta a taso mata keyarsa.

Magoya bayan Julian Assange lokacin da suka yi zanga-zangar adawa da tsare shi
Magoya bayan Julian Assange lokacin da suka yi zanga-zangar adawa da tsare shi

Magoya bayansa da dama, ciki har da sananniyar madinkiyar zamani Vivienne Westwood da budurwarsa Stella Moris, sun taru a harabar kotun gabanin sauraron shari’ar da safiyar yau Litinin.

Masu gabatar da kara a madadin gwamnatin Amurka, sun tuhumi Assange dan kasar Australia mai shekaru 49 da laifuka 18, na leken asiri da kuma amfani da komfuta ba bisa ka’aida ba, game da wallafa wasu bayanan sirri na sojojin Amurka shekaru 10 da suka gabata.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG