Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Junhuriyar Nijar za ta Inganta matakan tsaro don kare ma’aikatan aiyukkan kai jinkai


Women wait to receive baby food in Koleram, southern Niger, during the launch of a UN-backed feeding operation aimed at fighting malnutrition among young children.

Gwamtin Junhuriyar Nijar ta ce za ta inganta matakan tsaro bayan da wasu kungiyoyi masu alaka da kungiyar al-Qa’ida su ka yi barazanar far ma ma’aikatan jinkai.

Gwamnatin mulkin sojan Junhuriyar Nijar ta ce za ta inganta matakan tsaro don kare ma’aikatan agaji na kasa da kasa, bayan da aka sami rahoton barazana ga lafiyar ma’aikatan daga kungiyoyin da ke da alaka da al-Qa’ida. Jami’an aikin agaji sun ce barazanar za ta gurgunta kokarinsu na ciyar da mutane miliyan 8 da ke fama da yunwa a kasar ta Yammacin Afirka.

Da alamar dai barazanar ta fi karfi ne a yankin Maradi na kasar ta Nijar, da ke gabashin babban birnin kasar, Niamey, da nisan kilomita 600. Gwamnan Maradi, Kanar Garba Maikano, ya ce babu wani takamaiman bayani game da barazanar. To amman ya ce gwamnati na kokarin tantance kasashen dukkannin wadanda ba ‘yan Nijar ba da ke wannan yankin don ta samar da ingantattun matakan tsaro ga muhallinsu.

XS
SM
MD
LG