Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yajin Aikin Ma’aikatan Afrika ta Kudu


Yajin aikin ma’aikatan kiyon lafiya na Afrika ta Kudu ya bada dama ga mutanen da basa da wata horaswa su yi aikin wucingadi a assibitoci.

Mutanen da basa da wata horaswa a aiyukkan kiyon lafiya na tayin cewa a shirye suke suzo su yi aikin wucingadi a assibitocin Afrika ta Kudu don rage wahalhalun da za’a fuskanta a sanadin gagarumin yajin aikin da likitoci da sauran ma’aikatan kiyon lafiya ke gudanarwa yanzu a kasar. Tun kamar kwannaki ukku da suka gabata ma’aikata fiyeda milyan daya suke wannan yajin aikin. Haka kuma an aika likitoci na sojoji zuwa assibitocin jama’a fararen hula, yayinda kuma aka kwashe mutanen da suka fi fama da rashin lafiya daga assibitocin gwamnati zuwa assibitoci masu zaman kansu. Duk da cewa akwai wasu ma’aikata da ake dauka a matsayin “ma’aikatan da aikinsu ya wajabta” wadanda doka ma ta haramta musu yin yajin aiki, amma duk da haka ance wasunsu sun shiga yajin. Kuma yau Jumu’a ma ance an cigaba da bata-kashi tsakanin ‘yansanda da ma’aikatan dake yajin aikin, inda har ‘yansandan suka yi anfani da bututun feshin ruwa don tarwatsa gungjn masu zanga-zangar, har ma a bakin kofar wata assibiti ta Johannesburg.

XS
SM
MD
LG