Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ka-Ce Na-Cen Jami’an Tsaro Da ‘Yan Shi’a


Mata 'yan shi'a a lokacin da suke zanga zanga domin a sako shugabansu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky
Mata 'yan shi'a a lokacin da suke zanga zanga domin a sako shugabansu, Sheikh Ibrahim El-zakzaky

Sanarwar ta kara da cewa mutum uku sun mutu daga bangaren ‘yan Shi’ar yayin da wasu dakaru biyu suka  jikkata.

Rundunar sojin Najeriya ta ce arangamar da ta auku tsakaninta da mabiya mazhabar Shi’a ta faru ne sanadiyar hari da mabiya kungiyar suka kai wa dakarunta.

Wata sanarwa dauke da sa hannun kwamandan rundunar Garrison a hedkwatar sojin Najeriya, Major Gen. James Nyam, ta ce arangamar da ta faru a Zuba laifin ‘yan Shi’ar ne.

Ya kara da cewa sojoji na kan hanyarsu ta zuwa Kaduan za su kai makamai, sai mabiya Shi’ar suka tare hanya ba bisa ka’ida ba.

Rahotanni sun ce lamarin ya faru yayin da 'yan Shi'ar ke tattaki.

A cewar Gen. Nyam, masu tattakin sun yi yunkurin karbe makaman soji tare da farfasa motocinsu har da na fararen hula.

Ya kara da cewa ‘yan Shi’ar sun yi ta jifansu da duwatsu, lamarin da ya sa sojojin suka bude masu wuta.

Sanarwar ta kara da cewa mutum uku sun mutu daga bangaren ‘yan Shi’ar yayin da wasu dakaru biyu suka jikkata.

Sai dai bangaren na ‘yan Shi’a ya musanta wannan ikarari na sojojin.

“Mu yau tsawon shekaru 40 ba a san mu da amfani da makami domin cimma manufofinmu na addini ba, don haka babu yadda za a yi da rana tsaka wani ya zo ya ce muna amfani da makami. “ Inji Kakakin kungiyar na kasa Malam Ibrahim Musa.

Ya kara da cewa “na biyu kuma su jama’ar Zuba din ai shaidu ne, ai akwai bidiyon abubuwan da suka faru,” yana mai cewa babu yadda mara makami zai kai hari kan soja.

Rikici tsakanin jami’an tsaro da ‘yan mazhabar ta Shi’a ya jima yana faruwa tun bayan wata arangama da ta auku a shekarar 2015 inda har ta kai ga kama shugabansu Malam Ibrahim Al Zakzaky.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:03 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG