Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ka Yi Farar Dabara Da Ka Dawo APC, Buhari Ya Fadawa Matawalle


Shugaba Buhari, hagu da Gwamna Matawalle, dama yayin wata ziyara da ya kai fadar shugaban kasar a watan Fabrairu (Twitter/Matawalle)

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP wacce Matawalle ya hau mulki karkashinta, ta yi barazanar kalubalantar gwamnan a kotu.

A ranar Talata Matawalle ya koma jam’iyyar a hukumance inda gwamnoninta da dama ciki har da tsohon gwamnan jihar Abdulaziz Yari suka karbe shi a birnin Gusau.

“Ina mai alfahari da ka zabi wannan lokaci da farar dabarar da ka yi ta shiga jam’iyya mai mulki, sannan kofarmu a bude take ga ‘yan siyasa wadanda suka aminta da irin abin da muka sa a gaba wajen ciyar da Najeriya gaba.” Sakataren gwamnatin tarayya Boss Mustapha da ya wakilci Buhari a wajen taron ya ce.

“Yanke shawarar da ka yi bisa ra’ayin kanka ka shigo jam’iyyarmu, na nuni da cewa ajandarmu ta yin mulki na gari, ita ce dalilin da ya sa jama’a ke kara kwadaituwa da shiga jam’iyyar saboda daya zabin da suke da shi ya ki yin aiki.”

Shugaban na Najeriya ya kuma yi kira ga gwamnonin da ke mulki karkashin jam’iyyar, da ‘yan majalisu a sassan kasar, “da su ci gaba da yin aiki tukuru don jam’iyyar ta kara samun karbuwa, ta yadda za ta ci gaba da rike mulki har gaba da 2023,” a cewar wata sanarwa da kakakin Buhari Malam Garba Shehu ya fitar.

Matawalle da daukacin 'yan majalisar dokokin jihar da na kasa daga jihar, suka koma jam'iyyar ta APC daga PDP, illa mataimakin gwamnan jihar da wani dan majalisar tarayya daya.

Babbar jam'iyyar adawa ta PDP wacce Matawalle ya hau mulki karkashinta, ta yi barazanar kalubalantar gwamnan a kotu.

Yayin wani taron manema labarai da ya gudanar a Abuja, shugaban jam'iyyar ta PDP Uche Secondus, ya ce duk da sauya sheka da wasu gwamnoni suke sauya, babu abin da zai hana su lashe zaben 2023.

Secondus ya kuma zargi jam'iyyar ta APC da bibiyan gwamnonin jam'iyyarsu yana mai cewa APC ta ki ta fuskanci kalubalen da ke gabanta.

"Ban taba ganin kasar da tana fama da matsalar tattalin arziki da na tsaro ba, amma kuma ta mayar da hankalinta wajen zawarcin gwamnoni, wannan abin kunya ne." Secondus ya ce kamar yadda gidan talabjin na Channels ya ruwaito.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG