Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kabilar Bachama Ta Yi Barazanar Kai Najeriya Gaban Kotun Duniya


Gwamnan jihar Adamawa yayinda da ya ziyarci wani kauyen Bachama da rikicinsu da makiyaya ya shafa
Gwamnan jihar Adamawa yayinda da ya ziyarci wani kauyen Bachama da rikicinsu da makiyaya ya shafa

Kabilar Bachama na zargin sojojin sama na Najeriya da wuce makadi da rawa saboda wai sun zubawa kabilarsu ruwan bamabamai daga sama har suka hallaka mutane 75 amma kuma suka musanta in hakan

Su dai wadannan al’umman Bwate na kabilar Bachama da suka fito daga kauyukan Lawaru,Dong , da Bayan a karamar hukumar Demsa da kuma na kauyukan Nzoruwe,Pulum,Shaforon da Kodomti dake cikin karamar hukumar Numan sun bukaci gwamnatin tarayyar Najeriya data kafa kwamitin bincike mai zaman kansa domin hukumta wadanda ke da hannu a harin bom da suke zargin rundunan sojin samar kasar sun kai musu inda mutum 78 suka mutu a kwanaki.

Lamarin dai ya faru ne yayin da rundunar sojin saman ta je raba yayin rikici a tsakanin makiyaya da manoma a wadannan yankuna.

Da yake jawabi a taron manema labarai da suka kira, a Yola, shugaban kungiyar Farfesa Wunosiko Nzita ya ce suna bukatar rundunar sojin ta fito ta amsa laifin da aka aikata,da kuma bada hakuri amma ba musanta abun da ya faru ba.

Haka nan ya ce,su tuni suka shirya don gurfanar da dakarun sojin saman dama gwamnatin Najeriya,gaban kotun duniya ta ICC.

Su kuwa Mr Bosin Yakana, da Tony Mabulti sun bayyana hanyoyin da za’a bi domin a samu zaman lafiya musamman a tsakanin makiyaya da manoma a wadannan yankuna.

Tun farko ma dai sai da kungiyar Amnesty International ta fitar da wani rahoton ta inda ta soki rundunar sojin saman,yayin da ita kuma a bangarenta rundunar sojin saman ta fitar da nata martani a Abuja,inda ta musanta zargin. Wannan ma kuma na zuwa ne yayinda hankula ke soma kwantawa a wadannan wurare dake kudancin jihar Adamawan.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:41 0:00

Facebook Forum

Hawan Nasarawa, jihar Kano a Najeriya, lokacin da aka gudanar da bukukuwan Sallar Eid el Fitr
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG