Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

NDE Ta Kaddamar Da Shirin Koyas Da 'Yan Gudun Hijira Sana'o'i A Jihar Adamawa


Taron kaddamar da shirin horas da 'yan gudun hijira a Adamawa da NDE ta shirya

A wani sabon yunkuri na tada komadar 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya shafa,hukumar samar da aikin yi a Najeriya,NDE,ta kaddamar da wani sabon shirin koyawa yan gudun hijira sana’a,inda aka faro daga jihar Adamawa.

Shi dai ,wannan horo na ko cikin matakan da hukumar samar da aikin yi ta NDE,ke dauka a yanzu,don horas da 'yan gudun hijiran da rikicin Boko Haram ya shafa,inda sama da yan gudun hijira dubu biyu da dari biyar suka ci gajiyar shirin a Adamawa,daya daga cikin jihohin da balahirar Boko Haram ta fi shafa a Najeriya.

Yayin kaddamar da shirin,a sansanin 'yan gudun hijira dake Malkohi,kakakin majalisar dokokin jihar Kabiru Mijinyawa,ya ce tuni su a majalisar suka samar da doka domin kyautatawa wadanda tashe tashen hankulan Boko Haram suka shafa.

Mr Keneth Maigida shi ne shugaban riko na hukumar ta NDE a jihar Adamawa,ya yi karin haske game da wannan shiri na horas da 'yan gudun hijiran.

Shima Mr Midala Iliya,jami’in hukumar ba da agajin gaggawa, NEMA, a sansanin ya ce suna murna da wannan shiri na hukumar NDE.

Ahmad Abba Sudi da Shehu Muhammad Dankolo,da suka yi jawabi a taron sun shawarci yan gudun hijiran ne da su maida hankali wajen koyon sana’o’in domin kyautata rayuwarsu.

A saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG