Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kace Nace Tsakanin Gwamnan Jihar Bauchi Da 'Yan Majalisar Wakilan Jihar


Gwamnan JIhar Bauchi Barrister Muhammed Abdullahi Abubakar

A dangane da wannan yanayi, kungiyar sasanta rikici da kuma daidata tsakani ta gana da manema labarai a kokarin da take yi domin dinke barakar dake jam’iyyar APC a jihar Bauchi.

Kace nacen dake faruwa tsakanin ‘yan majalisar tarayya masu wakiltar jihar bauchi a gefe guda dakuma gwamnan jihar a daya bangaren na nuni da irin barakar da jam’iyar APC ke fama da ita a jihar.

Sanin kowane kafofin yada labarai musamman na cikin gida babu ranar da zata shige baka ji magoya bayan gwamnan jihar barrister Muhammed Abdullahi Abubakar suna maida martani game da korafi kokuma kage da akeyi daga bangaren ‘yan majalisun wakilan ba.

Comrade Nuraddin Muhammed Badamasi, shine ko’odinetan kungiyar, ya ce sun kira taron manema labarai ne domin su bayyana masu muradun wannan kungiya a karkashin jam’iyyar ta APC a jihar ta Bauchi.

Ya kara da cewa siyasa ra’ayi ce, kuma dole ne a sami sabanin ra’ayoyi, dan haka ne suka mike wajan sasanta duka bangarorin biyu.

A bangaren ‘yan majalisar kuma, Sani Muhammad Das, mai tallafawa honourabel Yakubu Dogara kakakin majalisar wakilai yayi bayanin cewa a bangarensu yadda zasu taimaki jama’ar jihar ne kadai a gaban su, lamarin da yayi sanadiyyar takun sakar da ake samu Kenan.

A bangaren gwamnan kuma, Comrade sabo Muhammad, mai taimakawa gwamnan a fannin labaru ya ce dukkan bangarorin biyu dan juma ne da dan jummai domin kuwa jam’iyya guda ce ta kafa su.

Ga cikakken rahoton Abdulwahab Muhammad Daga jihar Bauchi.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:33 0:00
Shiga Kai Tsaye

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG