Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kace Nace Tsakanin Zababbun Shugabannin Jihar Bauchi


BAUCHI: Gwamnan Bauchi M.A. Abubakar

Gwamnan jihar Bauchi Muhammad Abdullahi Abubakar ya fito fili karara yace dalilin rikicinsu da wasu ‘yan Majalisa masu wakiltar jihar shine sun bukaceshi da ya saya musu motoci da kuma gidaje a Abuja wanda yaki amincewa da bukatun.

Sai dai kuma a nasu bangaren ‘yan Majalisun sun karyata batun, inda suka bukaci gwamnan da ya fito da shaidar maganar da yayi.

A cewar gwamnan Bauchi Barista Mohammad Abdullahi Abubakar, “dalili kuwa shine mutanen nan akwai inda suka sameni, suka bukaci cewa a matsayina na gwamnnan jihar Bauchi zan saya musu gidaje a Abuja, zan kuma saya musu mota irin kirar Jeep. Na nuna musu nace koda kuwa muna kwanka cikin kudi, ba aiki na bane na saya musu gida ko mota domin su ‘yan Majalisar Tarayya ne….”

A mayar da martani a madadin ‘yan Majalisun Tarayya Sanata mai wakiltar Bauchi ta Kudu, Mallam Ali Wakili, cewa yayi idan mai magana wawane shi kuwa mai sauraro yana da hankali. Ya ci gaba da cewa wannan kage bai dace a ce ya fito daga shugaba ba, kuma yayi kalubale cewa mai mukayi, sai dai kuma kudin da yake kashewa yana cewa yayi gine gine ‘yan Majalisa ne suka amince da gwamnatin Tarayya taq baiwa jiha kudaden.

Saurari cikakken rahotan Abdulwahab Mohammad.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:56 0:00

An Sami Karuwar Farashin Kayayyaki A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:42 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Shiye-Shiryen Shiga Watan Azumi A Kasar Ghana
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Ziyarar Sakatare Blinken A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Al'umomi Sun Koka Game Da Tashin Farashin Kayayyaki
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:57 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG