Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

‘YAN NAJERIYA NACI GABA DA BAYYANA RAAYIN SU GAME DA CIKAN NAJERIYA SHEKARU 56


Bukukuwan Ranar Samun 'Yancin Najeriya.

Mutane naci gaba da bayyana raayoyin su game da cika shekaru 56 da Najeriya tayi da samun ‘yanci.

Hassan Umaru Tambuwal ya jiwo raayin wasu mazauna birbin Badun.

Da farko ga Muhammadu Sabiu da abinda yake cewa.

‘’Mun gode wa ALLAH tunda ya kaimu shekaru 56, tunda wadannan shekaru lafiya kuma muna cikin matsaloli da yawa na rayuwa, wato tsadar rayuwa da muka tsinci kammu ciki, wannan abu daga ALLAH ne amma yakamata shugabanni su duba su gani shin wannan cikas da ake ciki ina hanyar shawo kansu, domin yanzu yawancin duk da muke anfani dau cikin kasa shigo muna ake yi dasu.An rufe bakin iyaka, gashi dala tayi tsada, Sefa tayi tsada duk wadannan sun kawo sun jefa mu cikin hatsari, ga abubuwa nan na faruwa cikin majilisar kasa shugaban kasa na gani kamata yayi ya tsawata.’’

Ga Hassan Umaru Tambuwal da Karin bayani.2”34

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00

XS
SM
MD
LG