Accessibility links

Kada Matsaloli Na Wucin-Gadi Susa Mu Kauce Hanya-Shugaba Buhari.

  • Aliyu Imam

Shugaba Muhammadu Buhari na Najeriya.

Shugaban ya bayyana haka ne a jawabinsa na cikar Najeriya shekaru 56 da samun 'yanci.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yabawa 'yan Najeriya saboda sadauakr da kai da hakuri yayin da kasar take fama da mummunar komadar tattalin arziki.

Shugaba Buhari wanda yayi wannan yabo a jawabinsa na murnar cikar kasar shekaru 56 da samun 'yancin kai, yace yana sane da irin wahalhalu da 'yan kasar suke ciki, da suka hada da kasa biyan kudin makaranta, koma samar da abinci sdabod a tsadar shinkafa ko dangin hatsi.

Shugaban na Najeriya yace kada 'yan kasar su bari matsaloli na wucin gadi su sa su kauda fuska daga irin matakai na gyara da gwanati take dauka.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG