Kimanin mako guda da kaddamar da Kungiyar tsaro ta yankin Arewa da wasu kungiyoyin matasa su ka yi a Kaduna mai suna Shege-Ka-Fasa, al'ummar yankin na ci gaba da bayyana mabanbantan ra'ayoyi gameda irin wadannan kungiyoyin tsaro na yanki a Najeriya.
Kungiyar Dattawan Arewa da ake kira Northern Elders Forum a turance, ta ce ita ba ta ga laifin kafa irin wadannan kungiyoyi ba idan har za su bi doka.
Dr. Hakeem Baba Ahmed shi ne ya karanto sanarwar bayan taron Kungiyar Dattawan na Arewa, ya kuma bayyana ra'ayin cewa da alama sha'anin tsaro na kokarin fin karfin gwamnati.
A cewarsa, sha'anin tsaro ya tabarbare a dukkan bangarorin Najeriya, lamarin da ya ta'allaka da talauci da rashin aikin yi da yayi wa 'yan kasar katutu, da kuma ya wajaba a dauki matakin kawar da su.
Saidai ita Cibiyar binchike da bunkasa Arewa wato ARDP a turance, cewa ta yi kungiyoyin tsaron yankin ba su dace ba.
Dr. Usman Bugaje shi ne shugaban wannan cibiya wadda ta kaddamar da Kwamitin kwararru kan harkar tsaro don lalubo mafita a Arewa, ya ce kuma ba za su saka ido lamurran tsaro na tabarbarewa kuma su yi shiru ba.
Ga cikakken bayani daga Isah Lawal Ikara
Facebook Forum