Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kakakin Majalisar Wakilai Ya Lashe Kujerar Gwamnan Sokoto


Waziri Aminu Tambuwal gwamnan Sokoto mai jiran gado

Waziri Aminu Tambuwal kakakin majalisar wakilan Najeriya ya lashe kujerar gwamnan Sokoto.

Alhaji Aminu Waziri Tambuwal ya yi galaba ne akan Sanata Abdalla Wali na jam'iyyar PDP.

Tuni Sanata Abdallah Wali tare da jam'iyyarsa suka rungumi kaddara tare da taya murna ga wanda ya lashe zaben. Ambassador Wali ya yi fatan gwamnantin Waziri Tambuwal zata taimaka wurin cigaban jihar da yin alkawarin cewa zasu cigaba da bada tasu goyon bayan. Zasu bada shawarwari da duk hanyar da ta kamata saboda jihar ta cigaba.

Matakin da Ambassador Wali ya dauki ya farantawa Waziri Aminu Tambuwal rai kuma ya yi na'am dashi. Ya yabawa shi Wali din ya kuma kara da kiran duk 'yan takaran da suka fadi su fito su bada shawara idan suna da ita wadda zata taimakawa jihar ta cigaba.

Akan abun da sabon gwamnan zai fi ba fifiko da zara ya kama madafin iko sai ya ce babu shakka sha'anin ilimi zasu fara sa gaba. Bayan ilimi sai aikin gona da kiwon lafiya da yadda za'a samar ma jama'a aikin yi.

A jihar Kebbi ma dan takarar jam'iyyar APC Sanata Abubakar Bagudu ne ya ci zaben gwamna. Ya kayar da Janar Bello Sarkin Yaki na jam'iyyar PDP. Bagudu yace nasararsa ta mutanen jihar ce gaba daya. Su ne suka fito suka zabi gwamnatin da suke so.

A jihar Zamfara ma alamu na nunawa gwamna mai ci yanzu Yari na jam'iyyar APC ne zai kai labari gida.

Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:59 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG