Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalaman Shugaban Amurka Akan Korea ta Kudi Sun Janyo Shaci-Fadi


Shugaban Amurka Donald Trump
Shugaban Amurka Donald Trump

Kalamai masu zafi da rashin fayyacewa da Shugaban Amurka Danald Trump yayi a kan Korea ta Arewa, kafin ziyarar wannan mako da shugaban China Xi Jinping zai kawo a nan Amurka, sun janyo shaci-fadi akan cewa watakila yana niyyar daukar wani matakin da ko dai zai kai ga kulla wata babban yarjejeniya da China ko kuma ta janyo yaki gadan-gadan.

A wata hira da ya yi da jaridar London’s Financial Times a jiya Lahadi, Trump ya fada cewar idan China ba zata iya magance kalubaloli da Korea ta Arewa ke haifarwa ba, Amurka zata iya.

Ya kuma lura da cewa China tana da ikon fada a kan Korea ta Arewar, saboda haka ya yi kashedi cewar ya kamata China ta gaggauta sasanta matsalolin makaman nukiliya da na makamai masu lizzami na Pyongyang, idan kuma bata yi ba, a cewarsa, Amurka zata dauki matakan da “ba zasu haifar wa kowa Da mai ido ba.”

Dakatar da shirin makaman nukiliya da kuma hana gwamnatin Kim Jong Un daga kera makaman nukiliya mai cin dogon zango na kasa da kasa wato ICBM da zai iya kaiwa kan a bangaren Amurka, ana sa ran zasu kasance cikin muhimman batutuwan da shugaba Trump da takwararsa Xi zasu tattauna a ganawa da zasu yi a Mar-a-Lago dake Florida a ranar Alhamis.


Ziyarar da sakatarorin harkokin wajen Amurka Rex Tillerson da na tsaro James Mattis suka kai a wannan yanki a kwanannan ya taimaka ainun wurin tabbatarwa shugabanni a China da Tokyo da kuma Korea ta Kudu cewar Amurka zata ci gaba da daukan matakan takunkumin tattalin arziki wajen horad da Korea ta Arewa don ta chanja halayenta da kuma dakatar shirinta na kera makaman nukiliya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG