Accessibility links

Kalamun da Dr Idi Hong ya yi kan wuyar yin zabe a jihohin dake cikin dokar ta baci sun jawo cecekuce a jihohin da abun ya shafa.

Kalamun tsohon karamin ministan kiwon lafiya Dr Idi Aliyu Hong bai yiwa jihohin dake karkashin dokar ta baci dadi ba.

A cikin kalamunsa Dr Idi Hong ya ce bai dace a yi zabe a jihohin dake karkashin dokar ta baci ba musamman idan ana cigaba da tashin hankali. To sai dai gwamnan jihar Adamawa Murtala Nyako ya mayarda martani ta bakin daraktan watsa labaransa Ahmed Sajo inda ya ce sun yi mamaki da kalamun Dr Idi Hong musamman daga bakin irin wadanda suke ikirarin suna kaunar jiharsu. Gwamna Nyako ya ce irin su Dr Idi Hong 'yan koren shugaban kasa ne masu da'awar sai shugaban kasa ya sake cin zabe ko ta halin kaka. Amma yanzu sun fahimci cewa al'amarin ba zai zo masu da sauki ba. Don haka suna yin kemfen ne su tabbatar cewa jihohi uku masu kuri'u fiye da miliyan bakwai basu yi zabe ba. Idan babu wadannan kuri'un suna ganin shugaban kasa zai iya cin zabe. Amma basu san cewa ba sai sun nufi 'yanuwansu da muguwar niya ba kafin su cimma bukatunsu.

Haka ma shugabannin ma'abotan kafofin masu yada labarai sun yi taro inda suka yi allawadai da kalamun tsohon ministan. Shugaban kungiyar Alhaji Baba Iyali Kawu ya ce yana kira ga irin Dr Aliyu Hong su samarma jihar Adamawa zaman lafiya. Shi ma mataimakin shugaban kungiyar Mr. John D Luka kira ya yi ga 'yan siyasar jihar da su rika yin tunanin irin abubuwan da kalamunsu ka iya jawowa.

Ibrahim Abdulaziz nada karin bayani.

XS
SM
MD
LG