Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kalubalen Da 'Yan Najeriya Suka Fuskanta Kafin Su Tsere Daga Ukraine


Yan Najeriya a Ukraine
Yan Najeriya a Ukraine

A ranar Laraba hukumomin Najeriya suka kaddamar da shirin kwaso 'yan kasar da suka makale a kasashen Romania, Poland, Hungary da Slovakia da ke makwabtaka da Ukraine.

Daliban Najeriyar masu karatu a kasar Ukraine da Rasha ke kaiwa farmaki sun bayyana cewa har zuwa yanzu akasarinsu na zama dar-dar ne a kan abin da kan je ya dawo tun da bangarorin biyu basu cimma yarjejeniyar tsagaita wuta tsakanin juna ba.

Kusan mako daya tak da kasar Rasha ta mamayi Ukraine da hare-hare bayan ta sha musanta shirin far wa Ukraine a baya, dalibai yan asalin Najeriya da suka je karatu can na ci gaba da bayyana irin mumunar yanayin da su ke ci gaba da shiga duk da cewa gwamnatin Najeriya ta fara kwaso kwaso 'yan kasarta da suka makale a tsakiyan rikicin na kasashen biyu.

Rahotanni na kara fitowa a kan yadda ake nuna wariyar launin fata ga bakake ciki har da yan Najeriya a kan iyakokin kasar Poland, Romania da dai sauransu kamar yadda daliba Amina Sadik ta shaida mana ta wayar tarho, ko da yake, hukumomin Ukraine sun musanta wadannan zarge-zarge.

“Mutane da yawa a border din suna jira ba’a bar su sun shiga ba, amma kuma ana barin fararen fata kamar ‘yan Ukraine da Turawa ana barin su shiga da bas bas da mota da kafa amma mu kuma babaken fata da ‘yan Indiya aka hana mu shiga…….”

Abdullahi dalibi ne a jami’ar Dnipro na kasar Ukraine, ya ce suna zaman dardar duk da cewa babu wani gagarumin farmaki da kasar Rasha ta kai kan birnin Dnipro din amma duk sa’o’i biyu ana jin karar jiniya wanda alama ce na tunatar da mutane akwai yiyuwar barazana dake tafe kuma su ruga zuwa neman mafaka a irin gine-ginen na karkashin kasa idan suka ji karan hari a kusa da su.

A wani bangare kuma, Fauziyya da ke zaman daliba a kasar Rasha ta ce an jibge motocin yaki a duk sassan kasar da ta ke karatun aikin likita wato Rasha inda ake kwantar mu su da hankali cewa duk matakan tsaro da aka dauka don nema mu su kariya ce idan aka gano yiyuwar wata barazana.

A cikin Najeriya kuwa, matasan kasar musamman a kafar Tuwita na dada yin kira ga gwamnati da ta gaggauta aikin zuwa kwaso 'yan kasar da suka makale a can musamman ma dalibai don gudun abun da ka je ya dawo.

Gwamnatin tarayyar Najeriya dai ta dauki matakai da dama don kare da dawo da ‘yan kasarta da suka makale a can tun farkon wannan rikici tsakanin Rasha da Ukraine, inda a ranar Laraba ma shugaban kasa Muhammadu Buhari ya amince da bayar da dala miliyan 8.5 ga ma’aikatun harkokin kasashen waje da ayyukan jin kai da ci gaban al’umma domin dawo da ‘yan Najeriya sama da dubu 5 da suka makale a can, kamar yadda karamin ministan harkokin waje Zubairu Dada ya bayyana.

An yi kokarin ji daga bangaren gwamnati kan yadda za ta gudanar da wannan aiki abin ya ci tura.

XS
SM
MD
LG