Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kama Wasu Bakaken Fata Biyu A Shagon Starbucks Ya Haddasa Zanga-zanga


Zanga-zanga a harabar Starucks dake Philadelphia
Zanga-zanga a harabar Starucks dake Philadelphia

Kama wasu bakaken fata biyu wai domin suna cikin shagon Starbucks inda ake shan shayi suna jiran wani ba tare da aikata wani laifi ba ya haddasa zanga zanga har sai da aka kori manajan shagon tare da neman gafara da shugaban kamfanin na kasa gaba daya ya yi

Shugaban kampanin shayin-zamani da ake kira Starbucks da turanci ya isa birnin Philadelphia a jiya Litinin, da zummar ganawa da wasu mutane biyu bakar-fatan Amurka da aka kamasu a shagon saida shayin na Starbucks a makon da ya gabata yayin da suke jiran abokinsu.


Batun kama mutanen biyu ya dauke hankalin al’ummar kasar biyo bayan baza hoton bidiyon a shafin Twitter a ranar Alhamis.


Hoton bidiyon ya nuna ana kama bakaken fatar su biyu cikin lumana, yayin da wani ma’abucin wurin shan shayin- wani farar fata, yake tambayar yan sanda laifin da suka yi. An ji kuma wani wanda yazo shan shayin shima yana bada shaidar cewa babu wani laifi da suka yi, a don haka ba a san dalilin da yasa aka kira musu 'Yansanda ba.


Rahotannin sun ce mutanen biyun suna zaune a shagon suna jiran mutum na uku, sai wani ma’aikacin shagon ya kira ‘yan sanda.


Yan sandan sun sake mutanen sa’o’i bayan kama su, amma ba'a bayyana ko su wanene mutanen ba.

Rahotanni daga yankin sunce an sallami manajan shagon a jiya Litinin, yayinda ake ci gaba da zanga zanga a harabar wurinda aka kama su.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG