Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru: Hadarin Jirgi Ya Hallaka Wani Kwamandan Soja


Wasu Sojojin Kamaru

Wani jirgi mai saukar ungulu mallakar dakarun kasar Kamaru ya fadi a kusa da arewa maso gabashin iyakar kasar da Najeriya, inda ya halaka kwamandan dakarun kasar ta Kamaru.

Janar Jacob Kodji ya rasu ne a wannan hadari da yammacin jiya Lahadi a kusa da kauyen Bogo da ke Kamarun, yayin da suke rangadin yankin, kamar yadda wani jami’in soji ya fada.

Shi dai Janar din shi ke jagorantar yakin da kasar ke yi da mayakan Boko Haram.

Hukumomin kasar sun ce akwai wasu jami’an soji uku a cikin jirgin, wadanda suma sun rasa rayukansu.

Rikicin Boko Haram wanda ya samo asali daga Najeriya, ya fantsama zuwa wasu kasashe makwabta da suka hada da Kamarun da Chadi da kuma Nijar.

Rikicin ya kuma yi sanadin mutuwar mutane sama da dubu 25, kana ya raba kusan mutane miliyan 2.3 da muhallansu, kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil adama da Majalisar Dinkin Duniya suka bayyana.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG