Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Ta Ce Ba Ta Kori 'Yan Gudun Hijrar Najeriya Ba


Shugaba Paul Biya
Shugaba Paul Biya

A ci gaba da kace-na cen da ake yi kan zargin korar 'yan gudun hijirar Najeriya da ake zargin kasar Kamaru da yi, sai Kamarun ta ce ita fa sam ba ta kori 'yan Najeriya ba.

Kasar Kamaru ta karyata rahoton Hukumar Kula da ‘Yan Gudun Hijira ta Majalisar Dinkin Duniya (UNHCR), mai cewa ta tisa keyar ‘yan gudun hijirar Najeriya da kuma ‘yan Najeriya masu nemar mafaka su wajen 400 tun daga watan Janairun wannan shekarar.

Amma ta ce ya zama dole a sauya wajen zama ga mutanen da su ka yi hijira zuwa wuraren da ‘yan Boko haram ke iya kai ma su hari.

Gwamnan Yankin Arewa Mai Nisa, wadda ke makwabtaka da tsohuwar tungar ‘yan Boko Haram, wato jihar Borno, Mijinyawa Bakari, ya ce babu wani dan gudun hijirar da aka tilasta masa barin Kamaru.

Ya ce kasarsa na mutunta ka’idar kasa da kasa da ta tanadi cewa idan ma za a maida mutum zuwa kasarsa dole ne a yi hakan cikin rashin hadari da kuma mutunci tare da tabbatar da cewa hakan shi ya fi kuma zai fi dorewa.

Sai dai gwamnan ya ce wasu daga cikin ‘yan gudun hijirar da su ka zauna nesa da sansaninsu da ke Minawao - musamman ma a yankin Logone da Chari, inda ‘yan Boko Haram ke iya kai hari cikin sauki - ya kasance dole a dauke su zuwa wurare mafiya rashin hadari.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG