Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru ta kaddamar da taron habaka kasuwanci


Manyan garuruwan kasar Kamaru na kasuwanci

Firayim ministan kasar Kamaru kuma shugaban gwamnati Philemon Yang ya kaddamar da taron habaka harkokin kasuwanci tare da kara dokoki 25 domin kawo saukin kafa kamfanonin kasuwanci a kasar.

Taron da Firayim Ministan ya jagoranta an yi shi ne a cibiyar kasuwancin, wato birnin Douala.

Yayinda yake gudanar da taron dokoki 25 aka kara musamman dokokin da suka shafi kirkiro kamfanoni ko masana'antu. An yi dokokin ne saboda taimakawa wadanda suke da bukatar bude kamfanoni ko masana'antu cikin kasar.

Taron ya yi nuni da cewa idan dan kasuwa yana da kimanin kudin Kamaru jaka dari ko nera dubu talatin da biyar da kudin haraji zai iya kafa kamfani ko masana'anta.

Firayim Ministan ya gayyaci 'yan kasuwa na gida da na kasashen waje su kara kaimi wajen kara habaka harkokinsu cikin kasar ta Kamaru da nahiyar Afirka baki daya.

Shugaban gwamnatin yace sun canza wasu dokokin kasar na kasuwanci domin kawo sauki. Yace yin hakan zai taimaka wurin habaka kasuwanci a kasar ya kuma sa masu saka hannun jari cikin kasar su shigo domin yanzu sun samu walwala.

Bugu da kari duk wani mai karamar masana'anta ko karamin kamfani gwamnatin kasar zata taimaka masu domin habaka harkokinsu. Haka zai tabbatar da cigaba mai dorewa cikin kasar. Masu zaman kashe wando su ma za'a taimaka masu su samu abun yi.

Daraktan ma'aikatar kasuwanci yace 'yan kasuwa su hada karfi da karfe domin fadada harkokinsu. Yace yin hakan ne zai karfafa 'yan ketare su saka hannun jari a kasar.

Wakiliyar Bankin Duniya tace taron zai karfafa masu sa hannun jari su shigo kasar su saka jari.

Ga karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:44 0:00
Shiga Kai Tsaye

Gobara A Jihar New York

An Yi Jana'izar Mutane 15 Da Suka Mutu A Gobara A Jihar New York
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sauyin yanayi : Yankin Sahel na Afrika

Yadda Sauyin Yanayi Ke Rura Wutar Rikici A Yankin Sahel
please wait

No media source currently available

0:00 0:12:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Nijar, Fulani, Wodaabe

Yadda Funalin Wodaabe Suka Gudanar Da Gasar Nuna Kyau A Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG