Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Boko Haram sun yiwa wani limami da iyalansa yankan rago a Kamaru


Shugaban kasar Kamaru Paul Biya

Wasu 'yan Boko Haram sun yiwa limamin garin Mano dake kusa da garin Kwalkwata a jihar arewa mai nisa cikin kasar Kamaru yankan rago tare da iyalansa

Cikin dare ne 'yan ta'adan Boko Haram suka shiga gidan limamin garin Mano dake jihar Arewa mai Nisa ta kasar Kamaru suka yi masa yankan rago tare da iyalansa.

'Yan ta'adan basu tsaya nan ba sai da suka sace shanu. Jami'an tsaro dake kusa da garin suna Kwalkwata ne garin da ya fi girma a yankin.

A garin Kwalkwata din ma maharan sun sace shanu masu yawa har da masu kiwonsu da suka yi awan gaba dasu.

Lamarin baya bayan nan na neman ya zama kalubale ga sha'anin tsaro a jamhuriyar Kamaru wadda a makon jiya ta yi ikirarin sake salon tsaro domin shawo kan 'yan Boko Haram.

Ga karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:22 0:00

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG