Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamaru Ta Roki Ma’aikatan Noma 20,000 Su Koma Aiki


Wani manomi yana aikin noman koko a kauyen Ntui, Kamaru.
Wani manomi yana aikin noman koko a kauyen Ntui, Kamaru.

Kamfanin Raya Kasa ta Kamaru CDC ta yi kira ga dubban ma’aikatan gonaki da suka tserewa rikicin yan awaren kasar da su koma bakin aiki.

Kimanin rabin ma'aikatan kamfanin 20,000 sun bar aiki a cikin shekarar 2018, saboda rashin biyan albashi da kuma munanan hare-haren da suke fuskanta daga masu tayar da kayar baya.

Kamfanin a makon da ya gabata ya ce ba shi da lafiya a dawo, amma ma’aikatan sun nuna shakku inda suka ce ya kamata a fara sake gina gidajen da aka lalata ko suka lalace dalilin rikicin.

Hukumar raya kasar Kamaru, ko CDC, ta ce tana son dubban ma’aikata su koma gonakin da suke aiki na Ayaba da Dabino, da kuma gonakin roba a yankin Kudu maso Yamma mai fama da rikici.

A ranar Litinin ne shugabannin katafaren kamfanin na gwamnati, na biyu mafi girma a Kamaru, suka ziyarci garuruwa da kauyukan yankin, don ganawa da ma’aikatan da suka tsere daga tarzoma a shekarar 2018 tare da neman su koma.

Shugaban kungiyar kwadago ta hadakar noma da hadin gwiwa na Kamaru Gabriel Mbene Vefonge, wanda ke cikin tawagar, ya ce hukumar ta yi alkawarin biyan ma’aikatan da suka koma aiki.

Rundunar sojin Kamaru ta ce ta fatattaki 'yan tawayen daga gonakin da kungiyoyi masu dauke da makamai ke amfani da su wajen horar da mayakansu.

A cikin shekarar 2018, yan tawayen sun umarci ma'aikata da su bar gonakin tare da gargadin cewa za a kai wa wadanda suka ki yarda hari.

Hukumomin kasar sun ce kungiyoyin da ke dauke da makamai sun datse yatsun ma’aikata da dama, da ake zargi da hada kai da gwamnati tare da kona daruruwan gidaje da makarantu da kuma masana’antu.

William Lekunja, ma’aikaci ne a wata gona a Meanja, ya ce ya tsere a shekarar 2018, kuma zai iya komawa ne kawai idan kamfanin ya inganta yanayin aiki da kuma yanayin rayuwa a kauyukan da rikicin ya lalata.

Gwamnatin Kamaru ta ce wasu tsoffin ma’aikatan kamfanin na bin bashin albashinsu na sama da shekaru biyu. Kamfanin dai ya sha alwashin mayarwa da ma’aikatan albashinsu, amma ya ce rigingimu da kaura daga ma’aikatan ya haifar da raguwar samar da kayayyaki da kasuwanci.

Amma gwamnati ta ce harkokin kasuwanci da kudaden shiga sun karu bayan kusan ma'aikata 2,000 sun koma aiki a shekarun 2021 da 2022.

Babban daraktan kamfanin CDC Franklin Ngoni Njie, ya ce idan sauran ma’aikata 8,000 suka dawo da siyar da kamfanin zai koma matakin da ya gabata.

Ya ce daga nan za su samu damar biyan albashi da sake gina gine-ginen da aka lalata.

Rikicin yan awaren Kamaru ya samo asali ne a shekarar 2016, lokacin da yankunan yammacin kasar masu magana da harshen Ingilishi, suka nuna rashin amincewa da nuna wariya da yawancin masu magana da harshen Faransanci na kasar suke yi musu.

Sojojin Kamaru sun mayar da martani tare da murkushe yan tawayen, inda suka dauki makamai suna ikirarin kare tsirarun masu magana da Ingilishi.

Majalisar Dinkin Duniya ta ce tun daga lokacin, rikicin ya yi sanadin mutuwar mutane 3,500 tare da raba wasu 750,000 da muhallansu.

Moki Edwin Kindzeka ne hada wannan rahotan daga kasar Kamaru.

XS
SM
MD
LG