Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Apple Ya Sami Izinin Gwajin Mota Mai Tuka Kanta


Kamfanoni daban daban suna ci gaba da nazartar kirar motoci masu tuka kansu

Kamfanin Apple ya sami izinin gwajin motoci masu tuka kansu a kan titunan jihar California, wanda ya shiga jerin kamfanonin kimiyya dake wannan gwaje gwaje.

Ma’aikatar kula da motoci ta jihar California ta bayyana a ranar Juma’a cewar ta baiwa kamfanin damar gwada motoci guda uku da kamfanin Lexus ya kera.

Manyan jami’an kamfanin na Apple sun dade suna tararrabin ko kamfanin zai shirya shiga cikin gasar tseren kirar kimiyyar motar da ke iya tuka kanta.

Kamfanin da ke zaune a California bai bada wani Karin bayani dangane da izinin ba, sabanin nuni da wasikar da kanfanin ya aika a shekarar da ta gabata ta nuna ra’ayi kan kirar kimiyyar motocin masu tuka kansu.

Kamfanin na Apple dai shine na baya bayan nan wajen shiga filin gwajin motocin marasa direba, wanda kamfanoni kimanin 29 tuni suna da izinin gwajin kimiyyar a California. Wanda ya hada da Mashahurin kamfanin nan na kimiyya wato Google da kuma kamfanoni da suke kera motoci da suka hada da Ford da General Motors da BMW da Volkswagen da kuma Tesla.

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG