Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An kashe mutane kusan 60 a Iraq


Jami’an gwamnati a Iraki sun ce a kalla mutane 59 ne su ka mutu, a wani harin kunar bakin waken da aka kai a wurin da ake daukar sabbin sojoji a birnin Bagadaza.

Jami’an gwamnati a Iraki sun ce a kalla mutane 59 ne suka rasa rayukkansu, sannan kuma wasu 125 su ka sami raunuka, a wani harin kunar bakin waken da aka kai a wurin da ake daukar sabbin sojoji dake a birnin Bagadaza. Wani jami’in Ma’aikatar Harkokin Cikin Gida, ya ce maharin ya auna kuratan sojojin ne a yau Talata. Ana daukan harin a matsayin wanda ya fi muni tun farkon watan Ramadan wanda aka shiga a makon jiya. Tashin bam din a tsohuwar Ma’aikatar Tsaro na zamanin Saddam Hussein, shi ne na baya-bayan nan a jerin hare-haren da ake kaddamarwa don a auna karfin jami’an tsaron Iraki, a daidai lokacin da sojojin Amurka ke shirin barin Iraq a karshen wannan watan.

XS
SM
MD
LG