Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kamfanin Samsung Zai Tabbatar da Lafiyar Sabuwar Wayarsa


Sabuwar Wayar dake Kama Wuta
Sabuwar Wayar dake Kama Wuta

Hamshakin kamfanin kayan lantarkin Koriya ta Kudu wato Samsung ya bayyana cewa “ Yana kan hanyar shirye shiryen gyaran mafiya yawancin wayar hannun nan mai suna Galaxy Note 7 domin tabbatar da lafiyarta.

Da safiyar Litinin ne kamfanin dillancin labarai na Koriya ta kudu Yonhap ya ambaci wani kamfani mai samarwa da kamfanin Samsung kayayyaki yana fadin cewa kamfanin ya dakatar da kera wannan samfurin wayar hannu mai suna Galaxy Note 7 tare da hadin kan jami'an kula da lafiyar kayayyakin da ake sayarwa da jama'a a kasashen Koriya ta Kudu da Amurka da kuma China. Wannan ya biyo bayan rahotannin dake cewa manyan kamfanonin tallar wayoyin hannu na Amurka sun dakatar da sauyawa jama'a sabbin wayoyin na Note 7 domin maye gurbin tsoiffi a saboda fargabar cewa sabbin ma suna iya kamawa da wuta.

Tambarin kamfanin Samsung
Tambarin kamfanin Samsung

Janye wayar Galaxy Note 7 daga kasuwa da kuma yadda kamfanin Samsung ya tafiyar da wannan batun sun jefa shi cikin rikici mafi muni da ya taba gani cikin shekaru masu yawa. Hamshakin kamfanin dai na Koriya ta Kudu ya sha fama da kakkaucewa matsalolin wayar sakamakon kamawa da wuta da takeyi tun farkon lokacin da aka saki wayar a kasuwa a watan Agusta. Kamfanin ya bayyana cewa batirin wayar ke da matsala hakan tasa aka maida kusan wayoyi Miliyan 2.5 a watan Satumba, Amma rahotanni sun nuna wayoyin da aka sauya din suma suna kamawa da wuta.

Hotunan konannun wayoyin dai ya mamaye kafofin sada zumunta na internet, inda wadanda suke dasu suke bayyana cewa haka nan wayar ta kama da wuta.

A kwanan nan Jirgin saman Southwest Airlines ya kwashe fasinjojinsa sakamakon Hayaki da sabuwar wayar ta Note 7 din ta fara yi.

XS
SM
MD
LG