Accessibility links

Kamfanoni a Jihar Gombe Sun Soma Tallafawa Nakasassu


Gwamnan jihar Gombe Ibrahim Dankwambo
Yayin da gwamnatoci da hukumomi a Najeriya ke neman hadin kai da kungiyoyi masu zaman kansu domin samarda abun more rayuwa ma nakasassu sai gashi a jihar Gombe wasu kamfanoni sun soma bada irin wannan taimakon.

Yanzu dai kamfanoni guda biyar ne suka yi yunkurin tallafawa. Kamfanonin sun mikawa makarantar kurame da makafi katifu sama da dari biyu. Umar Barambo wakilin kamfanonin yace tun can farko kamfanonin suka yi alkawarin taimakawa ganin cewa makarantar ta nakasassu ne kuma iyayensu basu da karfi dalili ke nan suka tashi su bada nasu gudunmawar. Yace mutane ne dake da lalura a jikinsu kuma wuraren kwanciyarsu na bukatar taimako.

Onarebul Barambu yace kamfanonin guda biyar yanzu sun amsa kiran gwamna jihar Ibrahim Hassan Dankwanbo wanda ya sha kiran kamfanoni da kungiyoyi su tashi su hada hannu da gwamnati su taimaki haba harkokin ilimi musamman ilimin nakasassu. Ya kira sauran kamfanonin su bi sawun wadannan guda biyar domin idan ba a Gombe ba babu inda za'a ba kamfani fili ya kafa masana'anta ta sarafa kaya ya sayar kana ya yi shiru da bakinsa.

Kungiyoyin nakasassu na jihar sun kalubalanci sauran kamfanonin da 'yan siyasa da masu hannu da shuni su tallafawa gwamnatin jihar Gombe wurin inganta rayuwar nakasassu. Shugaban kungiyar Umar Goro yace kafin a kawo tallafin makarantar tana cikin wani mawuyacin hali. Yace sun dade suna kuka kafin a yi yunkurin dauketa zuwa Dahu lamarin da zai kara ma wadanda ke kauyuka wuyar zuwa makarantar. Yace to amma Allah ya ji kukansu kuma sun ji dadi domin ba za'a dage makarantar ba. Yace yanzu sun sa idanu su gani 'yan siyasa da duk wadanda suka san su 'yan Gombe ne me zasu yiwa nakasassu. Yace duk kamfanonin da aka ba kwangila zasu bisu su tambayesu me zasu yiwa nakasassu. Yace basa son nakasassu su cigaba da bara.

Banda taimakon da matar gwamnan jihar ta baiwa makarantar babu wani ko wasu da suka taba taimaka mata.

Ga karin bayani.

XS
SM
MD
LG