Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Dalilan Da Suka Sa Na Yi Murabus - Mataimakin Gwamnan Kano


Farfesa Hafiz Abubakar, Mataimakin Gwamnan jihar Kano yayin wata ganawa da ya yi da Muryar Amurka a lokacin da ya zo ziyara Amurka
Farfesa Hafiz Abubakar, Mataimakin Gwamnan jihar Kano yayin wata ganawa da ya yi da Muryar Amurka a lokacin da ya zo ziyara Amurka

"In Sanar da Alummar jihar Kano cewa, Ni Hafiz Abubakar na mikawa Mai girma Gwamnan jihar Kano Takardata ta Sauka Daga Mukamin Mataimakin Gwamnan Kano."

Mataimakin gwamnan jihar Kano, Prof. Hafiz Abubakar, ya yi murabus daga mukaminsa.

Prof. Hafiz ya mika takardar murabus din a wata wasika da ya aikewa gwamna Umar Ganduje a jiya Asabar, wacce ya wallafa a shafinsa na Twitter.

"Ina Sanar da Alummar jihar Kano cewa, Ni Hafiz Abubakar na mikawa Mai girma Gwamnan jihar Kano Takardata ta Sauka Daga Mukamin Mataimakin Gwamnan Kano. " Inji Prof Hafiz, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.

Daga baya kuma, mataimakin gwamnan ya wallafa wasikar da ya aikewa gwamna Ganduje.

"Mai girma gwamna, na so a ce na zauna har zuwa karshen wa'adinmu, domin mu cika burinmu na biyawa al'umar jihar Kano bukatunsu kamar yadda muka yi musu alkawari a lokacin zabenmu na 2015."

Wasikar wacce ke dauke da tambarin alamar cewa ta shiga hannun gwamnan, ta kara da cewa "amma saboda dalilai da suka shafi yadda ake tafiyar da harkokin gwamnati da muke samun sabanin ra'ayi.... ban yi adalci ga al'umar jihar Kano da kai kanka shugaban wannan gwamnati ba, idan na ci gaba da zama akan mukamina."

A 'yan makwannin nan da suka gabata, gwamna Ganduje da mataimakinsa Prof. Hafiz sun yi ta samun sabani kamar yadda rahotanni suka rika nunawa.

Masu fashin baki a fannin siyasa na cewa, akwai alamun Hafiz zai koma jam'iyyar PDP ne, ko da ya ke bai ambaci hakan ba.

Wannan shi ne karo na biyu da wani mataimakin gwamnan a Najeriya ya yi murabus daga mukaminsa cikin watanni uku.

A karshen watan Mayun da ya gabata, mataimakin gwamnan jihar Bauchi, Nuhu Gidado shi ma ya fice daga gwamnatin Muhammed Abubakar, bisa dalilin cewa babu yanayi da zai iya gudanar da aikinsa cikin kwanciyar hankali.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG