Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kano Ta Shiga Jerin Jihohi Masu Coronavirus


Rahotanni daga Najeriya na cewa, an samu mutum na farko da ya kamu da cutar coronavirus a jihar Kano da ke arewacin kasar.

Sabbin alkaluman da hukumar kare yaduwar cututtuka ta NCDC ta fitar a daren Asabar, sun ambato Kano cikin sabbin mutanen da aka samu dauke da cutar.

“Cikin mutum 13 da aka gano, 11 a Legas suke, daya a Delta, daya a Kano,” kamar yadda shafin yanar gizon na NCDC ya nuna.

Jaridar yanar gizo ta Daily Nigerian ta ruwaito cewa, a wani fitaccen asibiti mai zaman kansa aka gano mutumin da ke dauke da cutar a jihar ta Kano.

Alkaluman na baya-bayan nan na zuwa ne bayan da aka samu karin mutum 13 da ke dauke da cutar a duk fadin kasar.

NCDC ta kara da cewa, “yanzu jihohi 19 ne aka tabbatar suka samu bullar cutar a Najeriya.”

Najeriya na da mutum 318 masu coronavirus, an sallami 70 sannan 10 sun mutu, a cewar hukumar ta NCDC.

Facebook Forum

An Ga Watan Azumi A Najeriya - Sultan

Mai Alfarma Sarkin Musulmi Muhammada Sa'ad Abubakar Ya Ba Da Sanrwar Ganin Watan Ramadan
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:21 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
Wani Sirri Da Tsohon Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou Ya Fadawa ‘Sarki Sanusi II’
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:23 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

An Kai Wa Ofisoshin Kungiyar Ba Da Agaji Hari A Arewa Maso Gabashin Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:02 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG