Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karancin Kudi Ya Hana Zaben Kananan Hukumomi a Taraba


People thump print ballot papers during gubernatorial election in Kaduna, Nigeria, Thursday, April 28, 2011. Two states in Nigeria's Muslim north voted Thursday for state gubernatorial candidates after their polls were delayed by violence that killed at

A jihar Taraba ana cigaba da cecekuce dangane da rashin gudanar da kananan hukumomin. Fiye da shekara guda Kenan da nada shugabannin rikon kwarya ko kuma kantomomi a kananan hukumomi 16 da ke jihar.

Wani abu da ya janyo sabuwar takaddama shi ne rantsar da shugabannin da gwamnan jihar Darius Dickson Ishaku ya yi a kwanan nan.

Sai dai wannan mataki bai yiwa mutane da dama dadi ba ciki har da wasu daga jam’iyar ta PDP.

Amma gwamnatin jihar ta ce karancin kudi ne ya hana ta gudanar da zaben, wanda ta ce muddin har in za ta yi, za a yi watanni biyu ba a biya ma’aikata albashi ba.

Jihar ta Taraba mai yawan mutane kusan miliyan uku na karkashin mulkin jam’iyar PDP ne.

Domin jin bahasin kowane bangare dangane da takaddamar ta rashin gudanar da zaben kananan hukumomi, saurari rahoton da wakilin Muryar Amurka Ibrahim Abdulaziz ya aiko daga Jalingo, babban birnin jihar:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:27 0:00
Shiga Kai Tsaye

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne

Dalilin Da Ya Sa Nake Sana’ar Sayar Da Shayi Duk Da Cewa Ni Kansila Ne - Dayyabu Lawal Bala
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:52 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Bikin Lasar Gishiri

Yadda Aka Yi Bikin Lasar Gishiri A Jamhuriyar Nijar
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:32 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG