Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Bayani Akan Bayyanar Shugaba Buhari a Sallar Jumma'a Yau


President Muhammad Buhari bayan sallar Juma'a yau

Bayan makonni biyu ba'a ganshi ya fito waje ba wurin gudanar da aikinsa ko aikin ibada, yau shugaban ya bayyana a Masallaci wurin sallar Juma'a

Wannan halartar sallar Juma'a da yayi yau babu shakka ta sauya tunanen 'yan kasa a kansa musamman wadanda suke cewa bashi da lafiyar da zai cigaba da mulkin kasar.

Akwai wasu ma da suka dinga kiran ko ya sauka daga mulki ko ya koma neman jinya ko kuma majalisar kasa ta tsigeshi daga mulki.

Bayan da aka ganshi yana raha da jama'a da suka halarci sallar, Muryar Amurka ta tattauna da wasu da suka zauna kusa da shugaban.

Wani amininsa Alhaji Isyaku Ibrahim yana mai cewa shugaban ya fara gaida Sani Zangon Daura dake kusa dashi sai shi kansa Alhaji Isyaku sai kuma limamin masallacin. Haka ma wasu mutanen sun zo sun gaisa dashi irinsu Shehu Malami.

Baicin hakan shugaban ya zagaya ya gaida jama'a.

Daya daga cikin wadanda suka halarci sallar tare da shugaban Sanata Abu Ibrahim ya bayyana damuwarsa da juyayin irin yadda 'yan Najeriya ke tayin tsegunguma da maganganu mara dadi dangane da halin da shugaban yake ciki, musamman wadanda suke cewa baya iya tashi da kansa sai an daga shi ko kuma ana bashi abinci ta wasu hanyoyi ba ta baki ba.

Sanatan yace kamarshi sun gaisa. Yayi maganar aure da suka yi ya kuma yi addu'ar Allah ya bada zaman lafiya..Baicin haka ya kira sunayen wasu sanatoci da dama.

Ga rahoton Umar Faruk Musa da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:14 0:00

Facebook Forum

Laftanar Janar Farouk Yahaya

Makasan Sheikh Goni Aisami Sun Bata Sunan Sojin Najeriya – Laftanar Janar Farouk Yahaya
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:11 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Shin da gaske NNPP ba ta yi wa Shekarau adalci ba?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG