Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin bayani akan harin Mubi


Jihar Adamawa

Yanzu an gano cewa dan kunar bakin wake ne yayi shigar burtu ya tada bam a cikin wani Masallaci garin Mubi

Masallacin da dan kunar bakin waken yakai har yau Talata ana kiransa Masallacin Madina a garin Mubi. Kafin a ankara dan kunar bakin waken ya tada bam din dake jikinsa yayinda mutane suke sallar asuba kuma kammala raka'a daya

Yawancin mazauna wurin 'yan kabilar Shuwa ne da suka fito daga jihar Borno sanadiyar rikicin Boko Haram. Yawancin wadanda suke cikin Masallacin 'yan Shuwa ne.

Wani ganao ya ce mutane da dama suka rasa rayukansu. Jami'an tsaro sun gallaza wurin suna taimakawa.

Shugaban karamar hukumar Mubi ta arewa Musa Ahmed Bello da aka fi sani da suna Ahmed Ajayi ya ce tuni aka garzaya da wadanda suka jika zuwa asibitin garin. Ya ce bisa ga yanayin gari ya kamata mutane suna kula. Su daina saurin mantuwa. Ya ce kawo yanzu mutane 15 zuwa 20 ne bam din ya kashe.

Ga rahoton Ibrahim Abdulaziz da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:02:09 0:00

Facebook Forum

Bidiyo

Yadda Wani Mutum Ya Mari Shugaban Faransa Emmanuel Macron
please wait

No media source currently available

0:00 0:00:37 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Marigayi TB Joshua
please wait
Embed

No media source currently available

0:00 0:01:27 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Bidiyo

Gidajen Rediyon Najeriya Sun Gana Da Jami'an Diplomasiyya Kan Rikicin Twitter
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:51 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG