Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Bayani Kan Rasuwar Pele


ယခင္ကမာၻ႕ဖလားဆု(ပံုစံ)အေဟာင္းရဲ႕ ပံုတူတစ္ခုကို ပီလီကိုင္ထားစဥ္ (ဇြန္လ ၁၊ ၂၀၁၆)
ယခင္ကမာၻ႕ဖလားဆု(ပံုစံ)အေဟာင္းရဲ႕ ပံုတူတစ္ခုကို ပီလီကိုင္ထားစဥ္ (ဇြန္လ ၁၊ ၂၀၁၆)

Ana dada samun karin bayani kan musabbabin rasuwar shahararren dan wasan kwallon kafan nan na kasar Brazil, Pele


Shahararren dan wasan kwallon kafa na Brazil Pele, wanda ya shahara a duniya, da farko, a matsayin matashi mai cin kwallaye, wanda kuma ya jagoranci tawagar kasarsa ta lashe gasar cin kofin duniya har sau uku, wanda ba a taba yin haka ba, ya rasu jiya Alhamis yana da shekaru 82 da haihuwa a duniya.

An kwantar da shi a asibiti a karshen watan Nuwamban da ya wuce, kuma likitoci sun fada a watan nan na Disamba cewa yana fama da ciwon daji wanda ya karu tare da ciwon koda da zuciya. A watan Satumban 2021, an yi masa tiyata don cire masa wani kari daga hanjinsa.

Hukumar Asibitin Albert Einstein, inda aka yi jinyar Pele, ta fada a cikin wata sanarwa da ya fitar cewa ya mutu ne sakamakon raunuka a bangarorin jikinsa masu aiki.

‘Yar sa Kely Nascimento ta wallafa a shafinta na Instagram cewa “Duk abin da muke shi ne godiya gare ka, muna son ka har abada, Allah ya jikanka.”

XS
SM
MD
LG