Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Bayanin Kafa Dokar Hana Fita a Gombe


Gwamna Jihar Gombe Ibrahim Dankwambo.

Bayan da aka kusa samun tashin hankali a Gombe da safiyar jiya Asabar, hukumomi a Gombe sun yi maza sun kafa dokar hana zirga-zirga daga karfe uku na yamma zuwa kafe shida na safe.

Bayan da hukumomi su ka kafa dokar hana fita a Gombe, sanadiyyar wani yamutsin da ya kusa barkewa jiya Asabar, ‘yan kwanaki bayan markade wasu ‘yan BB da mota, hukumar ‘yan sandan jahar ta yi karin bayani ma Muryar Amurka.

Hukumar ‘yan sandan ta ce hukumomi a jahar Gombe sun kafa dokar hana zirga zirga daga karfe uku na yamma zuwa karfe shida na safe a duk fadin jihar. Hukumar ta yan sandan jahar, ta bakin kakakinta sufurtanda, Mary David Malum, ta shaida hakan biyo bayan hargitsin daya faru a sailin da ake shirin zuwa makabarta domin bisne yan kungiyar Boys Brigade da wani ma’aikacin Civil Defense ya taka su da mota a lokacin da su ka yi jerin gwano na bukukuwan Easter a ranar Lahadin daya gabata a garin Gombe.

A gafe guda kuma shugabannin addinai a jihar ta Gombe sun shiga gargadin matasa da su guje ma duk wani abun da zai kawo tashin tashina a tsakanin al’ummar Gombe. Reverend Abare Kalla ya yi kiran da a kai zuciya nesa saboda babu wani tashin hankalin da zai farfado da wadanda su ka mutu.

Shi kuwa Alhaji Usman Gurama, sakataren hukumar Alhazai, ya bayyana takaici dangane da faruwar hargitin na safiyar jiya Asabar, inda ya ce an kona masallacin dake gidansa.

Bincike dangane da batun na nuni da cewar yan kungiyar Boys Brigade guda 8 ne suka rasa rayukansu a yayinda shi matukin motar da ya janyo sanadiyyar mutuwar yan Boys Brigade din da abokinsa su ma kashe su.

Ga Abdulwahab Muhammad da cikakken rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:18 0:00


Facebook Forum

Shugaban Azman

Dalilin Da Yasa Muka Dakatar Da Tafiya Yajin Aikin Sufurin Jiragen Sama a Najeriya - Shugaban Azman
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Sojojin Najeriya sun samu nasarar kwace bindigogi sama da 500

Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Shugaban NDLEA a Najeriya, Janar Buba Marwa

Dalilin Da Ya Sa Muke Bin Diddigin Dukiyar DCP Abba Kyari - Buba Marwa
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:34 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya

Yadda Rikicin ‘Yan Aware A Yankin Kamaru Ya Shafi Wasu Al’ummoni A Najeriya
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:19 0:00
Karin bayani akan Bidiyo

Gwamna Matawalle

Dalilan Da Suka Sa Muka Sayi Motoci Ga Sarakuna A Zamfara - Gwamna Matawalle
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG