Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karin Mutum 187 Sun Kamu Da COVID-19 a Najeriya


covid
covid

Adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 ya kai 58,647 a Najeriya a cewar hukumar NCDC mai sa ido akan cututtuka masu yaduwa da daren ranar Talata, 29 ga watan Agusta.

Gaba dayan adadin wadanda aka tabbatar sun kamu da cutar COVID-19 a Najeriya ya kai 58,647 zuwa daren Talata, 29 ga watan Satumba, a cewar hukumar NCDC da ke sa ido kan cututtuka masu yaduwa.

A bayanan da ta ke fiddawa a kowace rana a shafinta na Twitter, hukumar ta NCDC ta ce an samu karin mutum 187 da suka kamu da cutar a ranar.

A cewar hukumar, cikin mutum 58,647 da suka kamu da cutar, mutum 49,937 sun warke kuma an sallame su daga asibiti yayin da mutum 1,111 ne suka mutu.

Hukumar ta kuma ce an samu karin adadin ne daga jihohi 13, ciki har da Jihar Legas da mutum 74. Sai kuma jihar Filato da ke biye da mutum 25.

Sauran jihohin sun hada da Rivers (25), Gombe (19), FCT (19), Osun (10), Kaduna (5), Borno (3), Ogun (2), Katsina (2), Nasarawa (1), Bayelsa (1), Edo (1)

Facebook Forum

Hira Da Dakta Faruk Bibi Faruk Akan Matsalar Tsadar Rayuwa A Najeriya Kashi Na Biyu
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:00 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG