Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Karon Battar 'Yan Manchester


Yaya Toure na Manchester City (dama) yana kokawar kwallo da Wayne Rooney na Manchester United a karawar battar da suka yi litinin 30 Afrilu 2012, a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester a Ingila, inda City ta doke United da ci 1-0.
Yaya Toure na Manchester City (dama) yana kokawar kwallo da Wayne Rooney na Manchester United a karawar battar da suka yi litinin 30 Afrilu 2012, a filin wasa na Etihad dake birnin Manchester a Ingila, inda City ta doke United da ci 1-0.

Manchester City ta doke abokiyar adawarta daga tsallaken gari, Manchester United ta koma sama a rukunin Premier na kasar Ingila

Duniya ta juya ta yi dadi ma 'yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester City, wadanda suka doke avokan adawarsu na tsallaken gari Manchester United da ci daya da babu a karon battar da suka yi litinin a gasar lig-lig na Premier na kasar Ingila.

A yanzu dai Manchester City ta koma sama, ita ce lambawan ana saura mata wasanni biyu ta kammala kakar wasannin bana. Idan har Manchester City zata iya doke Newcastle United wadda take ta biyar a Premier League da kuma Queens Park Rangers dake can kasa, to zata zamo zakarar Premier League ta bana, ko shakka babu.

Manchester City da Manchester United duka su na da maki 83-83, amma City tana kan gaba da rararn kwallaye 8.

Sauran wasannin Manchester United guda biyu, Swansea da Sunderland wadanda suke matsayi na 11 da 12 a teburin lig na Premier.

Wasan jiya litinin a tsakanin Manchester City da Manchester United ya kara jaddada ikirarin da wasu ke yi cewa bana dai, taurarin 'yan wasan City ne zasu haskaka. Vincent Kompany, dan wasan baya na City, shi ya jefa wannan kwallo kwaya daya tak da kai a bayan bugun kwana ana dab da tafiya hutun rabin lokaci.

Kuma har dawowa daga hutun rabin lokacin, 'yan wasan tsakiya na City sun hana 'yan United sakat, inda suka rika dafa ma masu kai hari, su na kum akomowa baya su na taya 'yan baya tsaron gida.

An ga manajan United Sir Alex Ferguson da na City Roberto Mancini su na zage-zage a gefen fili, har sai da aka shiga tsakani, amma daga karshe dai Mancini ne ya fice cikin filin da farin ciki.

XS
SM
MD
LG