Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasafin Kudin Bana Zai Taimakawa Yankin Da Rikicin Boko Haram Ya Shafa


Bayan tashin wani bom a Maiduguri, Yuni 22, 2015.
Bayan tashin wani bom a Maiduguri, Yuni 22, 2015.

Biyo bayan rattaba hannun da shugaban Najeriya, Mohammadu Buhari yayi ga kasafin kudin bana, yanzu gwamnatin kasar ta sha alawashin gudanar da ayyukan da ta kudiri aniyar aiwatarwa a cikin kasafin don farfado da komadar al’ummomin da rikicin Boko Haram ya shafa a Arewa maso Gabashin kasar.

Gwamnatin Najeriya ta lashi takobin taimakawa al’umomin yankin ta hanyar gyara musu muhallansu da gina gadoji da makarantu da kuma gyara hanyoyin da aka lalata.

Wannan yunkuri dai na daga cikin kasafin kudin bana da shugaba Buhari ya rattabawa hannu cikin kwanakin nan, batun da hadimin shugaban kasar ta fuskar ayyuka da tsare tsare Hon Ibrahim Hassan, yace akwai ayyuka da yawa da suka sami shiga cikin kasafin kudin.

Yanzu haka dai Majalisar Dattawan Najeriya ta fara zama domin jin ra’ayoyin jama’a game da batun kafa hukumar kula da farfado da yankunan Arewa maso Gabashin wato Northeast Development Commission.

Domin Karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:19 0:00

XS
SM
MD
LG