Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasafin Kudin Najeriya Kamar Akwai Lauje Cikin Nadi


Ngozi Okonjo-Iweala ministar kudin Najeriya

Tun kafin majalisun Najeriya su amince da kasafin kudin kasar gwamnonin jihohin arewa da masana kan harkokin tsaro suna ganin kasafin kudin na da wata manufa daban

A cikin kasafin kudin dake gaban majalisun kasar gwamntin tarayya ta kebe nera biliyan 50 domin tallafawa matasan 'yan tsageran Neja Delta su dubu talatin kawai.

Amma a kasafin gwamnatin ta ware nera biliyan 46 ma dakarun tsro da suka hada da sojojin kasa da na ruwa da na sama da ma 'yansanda. Wannan kudin da aka ware wa dakarun tsaro bai kai wanda aka ware wa 'yan tsagerun Neja Delta ba lamarin da ya sa gwamnonin arewa da kuma masana harkokin tsaro ke ganin kamar akwai lauje cikin nadi.

Gwamnan jihar Adamawa tsohon babban hafsan ruwa Murtala Nyako ya ce akwai abun dubawa game da kasafin. Ya ce wadanda suke tare da shugaban kasa babu abun da suke yi ila zalunci. Yadda kasafin yake ba'a yi adalci ba.

Dr Abdullahi Bawa Wase wani masani a harkar tsaro ya ce Neja Delta tana da hukuma na gashin kanta. Tana da ma'aikata mai zaman kanta a gwamnatin tarayya. Tana da kaso na musamman a kowane wata saboda 'yan tsageran yankin. Banda wadannan a sake daukan kudi har biliyan 50 a basu ya ce shi bai yi zaton Neja Delta ta ci wani bangaremn Najeriya da yaki ba kuma har duniya ta tashi ba zata iya yin haka ba. Basu kason gurbataccen tunane ne kuma wadanda suke ba shugaban shawara basa son shi.

Manjo Abu Jando wani tsohon jami'in fararen kaya ya ce watakila akwai wani abu da zasu yi masa. Idan ba haka ba bai kamata a ce kudinsu ya fi na jami'an tsaro ba. Ya ce kasafin kudin ai sai 'yan majalisu sun amince. Idan haka ne yaya ba zasu hango abun da ke faruwa ba. Zasu yi shiru ne kawai?

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:05 0:00
Shiga Kai Tsaye
XS
SM
MD
LG