Accessibility links

Daruruwan Mutane Suka Gudu Gada Kauyukansu a Jihar Adamawa


Wasu mutane da suka ji raunuka bayan harin 'yan bindiga da ake zaton Boko Haram ne a kauyen Chakawa ran 26 ga watan Junairu, 2014.

Yawan hare haren da kungiyar Boko Haram ke kaiwa kan kauyuka ya sa daruruwan mutane a wasu kauyukan jihar Adamawa suna gudu zuwa wasu wuraren.

Cikin 'yan kwanakin nan kungiyar Boko Haram tana kai hare hare kan kauyuka a jihohin Borno da Adamawa lamarin da ya yi sanadiyar ficewar wasu mutane daga kauyukansu a jihar Adamawa.

Daga kauyen Pitiku zuwa Cakawa da Sabon Garin Yandulum duk a karamar hukumar Madagali a jihar Adamawa 'yan bindiga sun yi mugun barna inda mutane fiye da dari biyar suka rasa gidajensu ban da asarar rayuka da dabbobi da dukiyoyi.

Mutanen da suka tsira suna korafin babu wani taimako da suka samu. Wani daga kauyen ya ce ya rokesu su kasheshi da bindiga sai suka ce sai dai da wuka. Wani ya ce su masu wannan aika-aikar su sani cewa ba aikin kirki suke aikatawa ba.

Ganin irin halin da mutane ke ciki ya sa gwamnatin jihar ta kafa kwamiti da zai taimakesu. Onarebul Hamza Bello kwamishanan harkokin iyaka shi ne shugaban kwamitin da aka nada. Ya bayyana wa mutanen cewa yanzu suna nazarin irin taimakon da za'a kawo masu. Nan ba da dadewa ba zasu ga taimakon gwamnati.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Najeriya ko NEMA a takaice ta bayyana rashin tsaro da cewa shi ke hana jami'anta kai agaji a wasu wuraren da abun ya shafa. Jami'in hukumar a jihar Adamawa ya ce idan sun samu tsaro suna iya zuwa su ga abun da zasu iya yi na taimako. Ya ce hanyar da mutum zai bi bai sani ba ko zai kai lafiya ba. Ya ce babban abun da ya damesu shi ne kada mutane su mutu domin rashin agaji a kan lokaci.

XS
SM
MD
LG