Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasafin Kudinmu Zai Fi Mai Da Hankali Kan Ayyukan Kasa - Trump


Shugaban Amurka Donald Trump yayin da yake magana a birnin Nashville dake jihar Tennessee

Fadar White House ta fitar da abin da ta kira kasafin kudin gwamnatin tarayya da zai ba da karfi kan Amurka.

Kasafin kudin na shugaba Donald Trump zai kara yawan kudin da ake kashewa kan harkokin tsaro, zai kuma sami kudin karin wajen zaftare kudin da ake kashewa kan wadansu ayyuka da ba su shafi tsaro ba.

Wannan fannin da za a zaftare sun hada da tallafin da ake bai wa kasashen waje, da cibiyoyin dake kula da ayyukan da suka shafi kula da muhalli.

A cikin wasikar da ya tura majalisa, shugaban kasar ya ce an yi kasafin kudin ne da nufin ba da fifiko kan harkokin tsaro domin idan babu tsaro ba za a sami ci gaba ba.

Kasafin kudin ya kunshi karin kashi 54 cikin 100 a fannin harkokin tsaro.

Za kuma a sami cikon kudin ne ta wajen zaftare kudade da ake kashewa a wadansu ayyukan na daban da ba su hafi tsaro ba.

Trump ya fada a cikin wasikar ta sa cewa, “mu na da zabuka mawuyata, kuma mun dade muna jan kafa a kai”.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG