Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Afghanistan ta Samu Sabon Shugaban Kasa


Sabon shugaban Afghanistan Ashraf Ghani a hannun dama da abokin hammayarsa Abdullah Abdullah a hannun haggu

Hukumar zaben kasar Afghanistan ta bayyana Ashraf Ghani a matsayin sabon shugaban kasa bayan shi da mai hammaya dashi Adullah Abdullah suka raftaba hannun akan yarjejeniyar aiki tare da raba madafun iko.

Hukumar zaben kasar Afganistan ta sanar da sabon shugaban kasar, ‘yan sa’oi bayanda manyan ‘yan takarar suka sa hannu a yarjejeniyar raba daunin Iko.

Da wannan yarjejeniyar Ashraf Ghani ya zama shugaban kasa, da kuma kirkiro da mukami wa abokin hamayyarsa Abdullah Abdullah. Yarjejeniyar ta bukaci Mr. Ghani ya dauki matakai nan da nan a matsayinsa na shugaban kasa, na surka ikonshi,domin sabon mukanin Mr. Abdullah ya dore.

Sanarwar ta biyo bayan kai komon siyasa da ake tayi tunda aka gudanar da zagaye na biyu a zaben shugaban kasa. Sai dai hukumar zaben bata fitar da yawan kuri’un da kowanne dan takara ya samu ba sabili da gudun kada yin haka ya tada fitina.

Ranar Litinin ishirin da tara ga watan Satumba ake kyautata zaton rantsar da Mr. Ghani.

XS
SM
MD
LG