Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Amurka ba ta Rage Taimakon da Take ba Najeriya Domin Cutar Kanjamau ba


 Boston Marathon
Boston Marathon

Ambasadan Amurka a Nijeriya, James Entwistle, ya tabbatar da dalilin da yasa Amurka ba zata dena bada taimako ga kasar domin cutar kanjamau ba ko da yake ya yarda cewa dokar Najeriya ta hana auren jinsi daya, ‘wata babbar damuwa ce.’

Ambasadan Amurka a Nijeriya, James Entwistle, ya tabbatar da dalilin da yasa Amurka ba zata dena bada taimako ga kasar domin cutar kanjamau ba ko da yake ya yarda cewa dokar Najeriya ta hana auren jinsi daya, ‘wata babbar damuwa ce.’

Yayinda shugabannin sauran kasashe na ikirarin dena bada taimako ga kasashen da suke goyon bayan wannan doka, kadan daga cikin su ne kawai suka aiwatar da wannan niyyar, duk da zargin da kungiyoyin yan ludu da madigo na duniya suke yi masu.

A farkon wannan watan ne shugaban kasa Goodluck Jonathan ya rattabawa wannan dokar wadda ita ce doka dake gaba da ludu da madigo mafi tsanani a duniya.

A karkashin dokar hana yin aure tsakanin jinsi daya, an ba shugabanni damar zartas da hukuncin shekara biyar zuwa 14 a gidan yari ga wanda aka kama da wannan aikata wannan, zama mamban kungiyoyin yan ludu, da kuma mutanen da suka halarci daurin aure na jinsi daya.

Jiya, Entwistle ya yi wannan magana a helkwatar ma’aikatar zabe ta kasa a Abuja.

Yayinda aka tambaye shi idan kasar Amurka zata rage taimakon da take ba Nijeriya sakamakon wannan dokar, Entwistle ya maida martani da cewa: “Hakika babu. Amma dole mu lura da ita sosai mu tabbatar da cewa dukan abinda muke yi yana bisa kan wannan sabuwar dokar.

“Kamar yadda kuka sani, muna sa miliyoyin daloli akan yaki da cutar kanjamau. Ni ba lauya bane, na karanta wannan dokar a gani na kamar wannan dokar tana iya sa takunkumi ga wadansu abubuwan da muke yi domin taimakawa wajen yaki da kanjamau a wannan kasar.

“Wadanan sune damuwoyin da muke dubawa yayinda muke duba dokar.” Ambasadan kuma yayi maganar kasarsa kan dokokin hana auren jinsi daya, yace, “Maganar auren jinsi daya tana kawo cecekuce kwarai ko’ina a duniya, har ma da kasata inda jihohi 17 daga cikin 50 suka amince da ayi. Wadansu suna cewa basu yarda da ita ba.”

“Bari in yi magana a matsayi na na abokin Nijeriya, wannan dokar kamar yadda muke gani, ta hana damar yin cudanya da juna da kuma damar tsayawa kana bin da mutum ke so, kuma a bisa ra’ayina, musamman ma a demokaradiya inda aka ci gaba, da zaran gwamnati ta fara Magana a kan irin wadannnan abubuwan, to an kayyade yancin yan’adam kenan. A gani na, wannan babban abin damuwa ne.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG