Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Burundi Na Shirin Ficewa Daga Kotun ICC


Burundi
Burundi

Majalisar Dokokin Burundi ta amince da wani kudurin doka da gagarumin rinjaye, na ficewar kasar daga jerin kasashen da su ka amince da halarcin Kotun Manyan Laifuka ta Duniya (ICC), na baya-baya nan a matakan ware kanta daga al'ummar duniya.

Bayan da Majalisar Wakilai ta kada kuri'ar amincewa da safiyar shekaran jiya Laraba, sai aka gabatar ma Majalisar Dattawa, inda aka amince da gagarumin rinjaye, wato dukkannin 'yan Majalisar 39 sun amince. Yanzu kudurin dokar na jiran Shugaba Pierre Bkurunziza.

Ko ma bayan kada kuri'ar da kasar ta yi ta ficewa daga ICC, dole sai gwamnatin kasar ta rubuta takarda ma Sakatare-Janar na MDD don bayyana niyyarta ta ficewa, kuma ficewar za ta fara aiki ne kawai bayan shekara daya da karbar wasikar.

"Zuwa yau dai ba mu karbi wata takarda mai nuna niyyarsu ba," a cewar mai magana da yawun MDD Stephane Dujarric. "Shakka babu, muddan mu ka samu irin wannan takardar, to zai zama abin takaici."

Ficewar Burundi daga kasashen da su ka amince da ICC, za ta zama ta farko a tarihin kotun ta ICC.

XS
SM
MD
LG