Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar China Ta Gargadi Amurka


Kasar China a yau juma'a tayi gargadi akan maka haraji akan sababbin kayan Amurka na kimanin dala biliyan sittin har idan gwamnatin Trump, ta ci gaba da barazanar ta ta kwannan akan cinikayya.

Ma'aikatar ciniki tace harajin da aka saka na kashi biyar cikin kashi dari zuwa kashi ashirin da biyar cikin dari a fiye da kayan Amurkadubu biyar da dari biyu an kimanta ne, kuma China tana da 'yancin maida martani a yakin cinikayya tsakanin manyan kasashen duniyar biyu.


Gargadin china ya zo ne jim kadan bayan Sakataren harkokin wajen Amurka Mike Pompeo ya hadu da Ministan harkokin wajen China Wang Yi a Singapore. Basu yi Magana da manema labarai ba bayan ganawar, an kuma bukaci manema labarai da su fita daga dakin kafin taron.


Jiya alhamis, ministan harkokin wajen China ya gaya ma manema labarai cewa Amurka na bukatar ta kwantar da hankalinta ta duba masu amfani da kayansu, inda yake Magana akan barazanar gwamnatin Trump na Karin haraji akan kayan china masu kimanin kudi biliyan dari biyu daga ainihin kashi goma cikin dari da kashiashirin da biyar cikin dari. Wang, ya kara da cewa wannan Karin harajin zai sa Amurka taji jiki akan kasuwancinsu dake China.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG