Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Girka Tana Tattaunawa da Kasashen Turai


Firayim Ministan Girka Alexis Tsipras a tsakiya

Yau Litinin jami'ai daga kasashe 19 masu amfani da kudin Euro suna gudanar da shawarwari dangane da kasar Girka.

Ganawar nada nasaba da yunkurin da suke yi na ganin kasar bata kasa biyan basussuka da suke kanta ba a karshen wannan wata.

Firayim Ministan Girka Alexis Tsipras yana gudanar da shawarwari a birnin Brussels tareda shugabannin asusun bada lamuni na duniya watau IMF, da na babban bankin Turai, da kuma na kungiyar tarayyar turai bayan da ya bayyana wani daftari na yarjejeniyar da ya kira "mai amfani da zai gano bakin zaren".

Shugaban kunigyar tarayyar turai Jean Laude Junicker, ya fada yau Litinin cewa sassan biyu suna kara samun fahimtar juna.

Shin PI Za Ta Fashe Kuwa Ko Yaudara Ce Kawai?

Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG