Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Indonesia Zata Hana Tafiye-Tafiye a Lokacin Azumin Ramadana


Kasar Indonesia zata hana mutane tafiye-tafiye a lokacin azumin watan Ramadana, yayin da take fuskantar yiwuwar karin masu kamuwa da cutar COVID-19 a kasar da ta fi yawan musulmai a fadin duniya.

Daga ranar Juma’a za a hana miliyoyin ‘yan Indonesia dake so su bar manyan birane zuwa hutu tafiya, a cewar gwamnatin kasar ranar Talata 21 ga watan Afrilu, wannan shine kwakkwaran matakin da gwamnatin ta dauka bayan da ta kasa shawo kan jama’a su zauna a gida don radin kansu. An sha caccakar kasar Indenosia akan yin sakaci a matakan da ta dauka tun da farko game da cutar, wadda da farko ta musanta cewa cutar ta bazu zuwa kasar.

Shugaban kasar Indonesia Joko Widodo, ya fadi cewa wani bincike da gwamnati ta yi kafin ta bada umarnin hana tafiye-tafiyen, ya nuna kashi 68 cikin 100 na mutanen kasar sun yarda ba zasu yi tafiya a watan Ramadana ba, amma kashi daya cikin hudu sun dage sai sun yi tafiya. Wannan yana nuna cewa har yanzu akwai adadi mai yawa, wanda ya kai kashi 24 cikin 100, a cewar Shugaban kasar a wata sanarwa da aka wallafa a shafin ma’aikatar yada labarai da sadarwa ta kasar.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG