Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kasar Italiya Na Shirin Girke Dakarunta a Jamhuriyar Niger


NIGER: Musa Changarai
NIGER: Musa Changarai

Kamar kasashen Amurka,Jamus, da Faransa dake da sojoji a cikin kasar Jamhuriyar Niger, ita ma kasar Italiya ta na shirin bin sawunsu da girke na ta dakarun domin su taimaka wajen yaki da ta'addanci.

Shafin labarai na wata jaridar 'yan Niger mazauna kasashen waje, ya ambato shugaban gwamnatin kasar Italiya Paulo Jantiloni yana bayanin cewa kasarsa ta dukufa wajen girke dakarunta a nahiyar Afirka.

Shugaban Italiyan ya yi bayanin ne ranar Laraba 13 ga wannan watan a can Italiya tare da cewa shirin zai fara ne da kasar Niger dake yammacin Afirka domin yakar ta'addanci da ya addabi yakin..Sojojin Italiya dari da hamsin za'a girke domin su horas da sojojin kasar dake fama da 'yan ta'adda.

Baicin horas da sojojin Niger, dakarun na Italiya zasu sa ido akan barauniyar hanyar da bakin haure ke anfani da ita suna kutsawa Turai.

Italiya ta bi sawun kasashen Amurka da Jamus da Faransa wajen girke dakaru a kasar Niger. Matakin amincewa kasashen waje su girke dakarunsu a kasar ta Niger ya jawo ayar tambaya daga wasu 'yan kasar.

Malam Alkasum Abdulrahaman mai bin digdigin kasashen duniya ya ce tun kafin shugabansu ya je Faransa aka soma jita-jitar cewa kasar Italiya za ta girke dakarunta a kasar, amma sai gashi shekaranjiya maganar ta tabbata. Ya ce shin kasashen dake zuwa Niger wani horo na musamman suke ba dakarun kasarsu da har yanzu bai yi tasiri ba? A cewarsa bisa wane ka'idoji suke "zamne a kasarmu?" Me suke biya na hayar filin kasar da ma sarararin samaniya?, inji Malam Alkasum.

Musa Changari na wata kungiya ya ce me ya sa gwamnatin ke ba kasashen waje damar girke dakarunsu ba tare da tuntubar 'yan kasar ba? A cewarsa wakilan jama'a ne za su amince da haka kamar yadda gwamnatin Italiya take bukatar amincewar majalisunta kafin ta tura dakarunta kasar Niger. A ganinsa yanzu tamkar kasar Italiya na shirin sayen kayan sata ne.

Sai dai ministan tsaron kasar Niger Kalla Mukhtari ya ce duk kasar da za ta taimaka masu yaki da makiyan kasarsu su na mara da ita. Bayan sun gama yaki da 'yan ta'adda to kowane sojin kasar waje aka gani ya na cin zarafin 'yan kasa zasu san yadda za su yi dashi.

Ga rahoton Souley Barma da karin bayani.

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:07 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG